W
WEB3 JOB CLASS
@WEB3JOBCLASS56 подп.
34просмотров
60.7%от подписчиков
4 января 2026 г.
Score: 37
MUHIMMIYAR SHAWARA GA TRADERS Domin samu nasara a Dex ko Degen trading, dole ne ka fahimci cewa wannan kasuwanci ne mai haɗari sosai, don haka ba a shigar shi da wasa ko greediness. Abu na farko da ya fi muhimmanci shi ne risk management, wato sanin yadda ake kula da jarin da ake da shi. Trader bai kamata ya saka duk kuɗinsa a trade ɗaya ba, ba tare da saka stop-loss domin samun kariya daga asara idan kasuwa ta juya akasin yadda take tafiya. Wani muhimmin abu kuma shi ne fahimtar liquidity da volume na token. Token da ke da ƙananan liquidity ko volume yawanci ba ya da kwanciyar hankali. Shiga trade da wuri ma na taka muhimmiyar rawa a Dex trading. Duk da haka, shiga da wuri ba yana nufin shiga ba tare da bincike ba. Trader ya kamata ya yi amfani da kayan aikin gano sabbin pairs, amma ya tabbatar da cewa token ɗin ba scam bane kafin shiga kasuwa. Shiga bayan jama’a sun riga sun yi cunkoso yawanci yana sa trader ya sayi token a saman farashi, wanda hakan ke jawo asara. Sanin lokacin fita daga trade yana da muhimmanci kamar sanin lokacin shiga. Trader bai kamata ya riƙa jiran riba marar iyaka ba. Yana da kyau a rika ɗaukar riba a hankali, ta hanyar sayar da wani kaso daga token, sannan a bar sauran a matsayin “free bag”. Idan volume ya fara raguwa ko alamun sayarwar dev suka bayyana, ya dace trader ya fita da wuri. Halin dev da al’ummar project (community) ma na da matuƙar tasiri. Project da ke da dev mai aiki da kuma community mai gaskiya yawanci suna da ƙarancin haɗari. Amma idan dev ya fara yin shiru ko kuma Telegram/X ya cika da bots, wannan babbar alama ce ta kowa ya gudu. A ƙarshe, trader ya kamata ya guji yin trading da emotion. Tsoro, kwaɗayi, da fushi suna janyo Asara a Dex trading. A taƙaice, nasara a Dex ko Degen trading tana buƙatar ilimi, risk management, haƙuri, da tsananin discipline. Duk wanda ya shiga Dex trading ba tare da waɗannan abubuwa ba, yawanci yana fuskantar asara. Jumma'at Kareem Dex Trader 4/01/2025
34
просмотров
1978
символов
Нет
эмодзи
Нет
медиа

Другие посты @WEB3JOBCLASS

Все посты канала →
MUHIMMIYAR SHAWARA GA TRADERS Domin samu nasara a Dex ko Deg — @WEB3JOBCLASS | PostSniper